Jami’an Kwastam sun kama manyan motoci 73 dankare da buhunan shinkafa da ganyen wiwi a jihar Ogun

Hukumar kwastam reshen jihar Ogun ta kama manyan motoci 73 da suka shigo kasarnan dankare da buhunan shinkafa 44,933 jihar.
Shugaban hukumar Bamidele Makinde ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar dake Idiroko a karamar hukumar Ipokia.
Makinde ya ce hukumar ta yi wannan kame ne daga watan Faburairu zuwa 6 ga Disembar 2022.
Ya ce a tsakanin wannan lokaci hukumar ta kama buhuna 41 da kulli 940 na ganyen wiwi.
Sauran kayan da hukumar ta kama sun hada motoci kiran ‘Tomas’ guda 99 wanda aka sako kayan a ciki, motoci guda 8, mota kiran ‘Wrangler 2020’ daya, manyan motoci na daukan kaya guda 8, compressors guda 31, galan 16,224 na man gyada da babura 19.
“Kayan gwanjo daurin dila 8,517 da wadanda ke buhuna 229, tayoyin mota 3,629, buhuna 4,700 na siminti, dauri uku na gwanjon jakunkuna da wasu guda 384, kayan 170 na Naman kaza, compressor na mota 192, kwali 2,250 na Kwayoyin tramadol, compressor na na’uran sanyi guda 222, gwanjon takalma 227, wasu takalma a buhuna 320 da wasu a katan 120, atamfa 485 da buhuna 302 na masara.
Bayan haka Makinde ya ce adadin yawan kudaden kayan da hukumar ta kama ya kai Naira Miliyan 4,886,647,634.92.