Iyorchia Ayu ba alheri ba ne, baƙin jinin sa ne ya janyo faɗuwar PDP zaɓen 2023 – Chimaroke Nnamani

Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya shawarci Iyorchia Ayu ya haƙura kawai ya sauka daga shugabancin PDP, tare da cewa, “rashin taɓuka abin kirki da PDP ta yi a zaɓen 2023, ƙarƙashin shugabancin Ayu, babbar asara ce da ba su da irin ta.”
Nnamani wanda yanzu haka Sanata ne, ya ce shugabancin Ayu ya haifar wa PDP rashin nasara, rashin albarka da baƙin jini, saboda sakaci, ƙwaɗayi da ƙetar Ayu.
Idan ba a manta ba dai PDP ta kori Nnamani daga cikin jam’iyyar a ranar 10 Ga Fabrairu, kafin zaɓen shugaban ƙasa. Dama kuma an dakatar da shi a cikin Janairu.
Nnamani ya ce Ayu gagarimar guguwar bala’i wadda ta yi wa PDP babbar illa.
“Ayu babban bala’i nesa ya sauka kan PDP. Abin da kawai ya rage a yanzu kawai a kore shi daga PDP.
“Ta yaya Ayu zai dogara da Sashe na 57 (7) na Dokar Jam’iyya, alhali kuma shi da kan sa ya take wannan sashe wajen dakatar da ni daga PDP?”
Saukar Ayu Daga Shugabancin
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Shugaban Jam’iyya Ayu ya sauka, an naɗa Umar Damagum riƙon ƙwarya
Rikicin PDP ya ci Shugaban Jam’iyya, Sanata Iyorchia Ayu, wata ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa
Ayu ya bi umarnin Babbar Kotun Jihar Benuwai, wadda a ranar Litinin ta yanke hukuncin cewa kada ya ƙara kiran kan sa Shugaban PDP, tunda shugabannin mazaɓar ƙauyen su sun dakatar da shi.
Majalisar Zartaswar PDP (NWC) ce ta kira taron gaggawa ranar Talata, inda ta ce ta bi umarnin Babbar Kotun Benuwai wadda a ranar Litinin ta dakatar da Ayu, bayan wani ya maka shi kotu, ya ce a tilasta dakatarwar sa, kamar yadda mazaɓar sa su ka ce sun yi.
NWC ya ce ya yi amfani da Sashe na 45 (2) na PDP dokokin 2017, ta naɗa Mataimakin Shugaba na Arewa, Ambasada Umar Damagum a matsayin shugaban riƙo daga ranar Talata, 28 ga Maris, 2023.
PREMIUM TIMES ta buga labarin dakatar da Ayu da kuma na umarnin da kotu ta ba shi na ya daina kiran kan sa shugaban PDP.
Gargaɗin Babbar Kotu Ga Ayu:
Kotu ta hana Iyorchia Ayu kiran kan sa Shugaban PDP.
Rikicin PDP ya ƙara muni, har ta kai Babbar Kotun Jihar Benuwai da ke Makurɗi ta umarci Shugaban PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, cewa ya daina kiran kan sa shugaban PDP tunda mazaɓar sa ta dakatar da shi.
Mai Shari’a W. I Kpochi ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin, cewa wannan umarni ne na wucin-gadi, tunda an dakatar da shi.
Mai Shari’a ya yanke hukuncin ne bayan wani ɗan jam’iyyar PDP a Jihar Benuwai, mai suna Terhide Utaan ya maka Ayu a kotu.
Utaan ya maka Ayu da PDP a kotu, sai dai waɗanda aka kai ƙarar ba su bayyana ba, kuma ba su tura lauyoyin su ba a kotun.
Hukuncin hana Ayu ci gaba da kasancewa shugaban PDP ya zo ne kwana ɗaya bayan reshen mazaɓar ƙauyen su ya fitar da sanarwar dakatar da shi daga mamba na PDP.
Kotu ta ce Ayu a yanzu ba shugaban PDP ba ne, daga yanzu har zuwa ranar da za ta yi hukunci tukunna.
Dakatar Da Ayu Daga PDP:
Shugabannin mazaɓar ƙauye sun dakatar da Shugaban PDP sukutum, Iyorchia Ayu daga jam’iyya.
Rikicin da ya tirniƙe jam’iyyar PDP bayan zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni, ya ɗauki sabon salo, yayin da shugabannin ita jam’iyyar a mazaɓar ƙauyen Igyorov cikin Ƙaramar Hukumar Gboko, su ka bada sanarwar dakatar da Iyorchia Ayu Shugaban PDP na Ƙasa baki ɗaya.
An dakatar da Ayu ne a ranar Lahadi, kamar yadda Sakataren Jam’iyya na ƙauyen su Ayu, mai suna Vangeryina Dooyum ya bayyana a madadin shugaban PDP na mazaɓar mai suna Kashi Philip.
Sanarwar ta ce sun dakatar da Ayu ne saboda sun kama shi ya na yi wa PDP zagon ƙasa, wato ‘anti-party’ a zaɓukan da aka gudanar a faɗin ƙasar nan.
“Mun lura a cikin baƙin ciki da damuwa cewa Iyorchia Ayu wanda shi ne Shugaban PDP na Ƙasa, ya kawo wa nasarorin da PDP ta kamata ta samu cikas a zaɓukan da su ka gabata a wanan mazaɓa ta Igyorov,” haka Dooyum ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar.
Sun zargi Ayu wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne da rashin taɓuka komai a zaɓen gwamna da PDP ta yi a jihar Benuwai.
“Bincike ya kuma gano cewa Ayu bai zo Benuwai ya yi zaɓen gwamna da na majalisar jihohi a ranar 18 Ga Maris, 2023 ba.”
PDP ta rasa kujerar gwamnan Benuwai, ta rasa sanatoci biyu da ta ke da su, kuma ‘yan majalisar tarayya 11 da ta ke da su. Dama ‘yan majalisa 12 na tarayya Benuwai ke da su. Yanzu da Gwamna da su ɗin duk APC ta lashe a jihar.
Dooyum ya ce binciken su kuma ya gano cewa yawancin makusantan Ayu duk APC su ka zaɓa, ba PDP ba, shi ya sa PDP ba ta taɓuka komai ba a mazaɓar da aka haifi Ayu.
“A kan haka mun a yanzu ba mu da yaƙini a kan cancantar iya shugabancin jam’iyya a hannun Ayu. Saboda haka mun dakatar da shi a matsayin mamba na PDP. Dakatarwar ta fara tun daga 24 Ga Maris, 2023.”
Primium Times ta tuntuɓi Sakataren PDP na Jihar Benuwai, Bemgba Iortyom, wanda ya ce ba shi da labarin dakatarwar sai a bakin wakilin mu.
Sai dai kuma ya ce shugabannin mazaɓa ne ke da ikon dakatar wa Mamba.
Tsakanin Ayu Da Ortom Gwamnan Benuwai
Tun bayan zaɓen Iyorchia Ayu ya sha fama da Gwamna Samuel Ortom na asalin jihar haihuwar Ayu.
Ortom na cikin gwamnoni biyar masu neman Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu, tunda PDP ta tsaida Atiku Abubakar ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Wannan rikicin ne ya sa gwamnonin biyar, Samuel Ortom, Nyesom Wike na Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Okezie Ikpeazu na Abiya da Seyi Makinde na Oyo ba su goyi bayan takarar Atiku Abubakar ba.
Idan za a iya tunawa, shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya bayyana yadda Ayu ya harzuƙa shi, har shi da mutanen sa su ka fice daga PDP, su ka koma ANPP.