Akalla mutum 7,806 suka kamu da cutar tarin fuka a tsakanin shekarar 2021 – 2022 a jihar Bauchi

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtukan kanjamau, tarin fuka, kuturta da zazzabin cizon sauro reshen jihar Bauchi Sani Mohammed ya bayyana cewa mutum 7,806 ne suka kamu da cutar tarin fuka a shekarar 2022 a jihar.
Mohammed ya fadi haka ne a taron ranar cutar ta duniya a garin Bauchi.
Ya ce jihar ta samu Karin mutum 2,154 da suka kamu da cutar a shekarar 2022 daga mutum 5,652 din da suka kamu da cutar a shekaran 2021.
A shekarar 2022 shine jihar ta fi samun yawan mutanen da suka kamu da cutar a cikin shekara daya.
“Zuwa yanzu mutum 5,518 dake dauke da cutar na amsar magani inda daga ciki mutum 5,192 sun warke.
“Akwai asibitin kula da masu fama da tarin fuka kyauta guda 798, wuraren yin gwajin cutar 127 a jihar Bauchi.
Domin dakile yaduwar cutar gwamnati ta hada hannu da kungiyoyin bada tallafi kamar ‘Breakingthrough Action-Nigeria’ domin gano mutanen da suka kamu da cutar.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kebe ranar 24 ga Maris domin cutar tarin fuka ta duniya.
Mohammed ya ce a taron bana gwamnati za ta wayar da kan mutane game da cutar a shirye shirye na talabijin da radiyo.
Ya ce gwamnati za ta yi wa mutane gwaji da basu maganin cutar kyauta sannan da bada magani da gwajin cututtukan Kanjamau, Korona, hepatitis da zazzabin cizon sauro.
Shugaban Shirin dakile yaduwar cutar tarin fuka ta jihar Bauchi Yakubu Abdullahi ya ce za su horas da jami’an lafiya domin gano cutar a jikin yara kanana.
Ya ce shirin ya hada hannu da asibitocin kula da yaran dake fama da yunwa dake jihar domin yi musu gwajin cutar.
“Gano tarin fuka a jikin yaro na da wahala inda hakan ya sa muka tsara hanyoyin yin gwaji da gano cutar.