‘INKWANKULUSIB’: Doguwa, Ɗan Majalisar da ake tuhuma da kisan kai ya lashe zaɓen Tudun Wada/Doguwa a Kano

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Ado Doguwa, kuma wanda ake zargi da laifin kisan kai a ranar zaɓe, Ado Doguwa, ya lashe zaɓen dabai kammalu ba, wanda aka kammala a ranar 15 Ga Afrilu.
Baturen Zaɓe Farfesa Sani Ibrahim, ya ce Doguwa ya samu ƙuri’u 41,573, shi kuma Yusha’u Salisu na NNPP ya samu 34,831.
An dai yi zaɓukan da ba su kammalu ba a mazaɓu takwas cikin Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.
Wakilin ya ruwaito cewa an samu ruɗani da firgita masu zaɓe a zaɓen na wanda bai kammalu ba a ƙaramar hukumar.
Wannan ne karo na biyar da Doguwa zai wakilci ƙananan hukumomin biyu, kuma ya na ta mafarkin ganin ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Rahotanni daga Kano sun tabbatar da NNPP ta ƙwace kujerar Majalisar Tarayya ta Ƙaramar Hukumar Fagge daga hannun Aminu Goro na APC.
Sannan kuma a Majalisar Dokokin Jihar Kano guda 40, NNPP na da 28.