Ina jiran El-Rufai ya aiko a kama ni din – Wabba

Shugaban Kungiyar Kwadago NLC Ayuba Wabba ya ce yana jiran gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya aiko a kama shi kamar yadda ya sanar.

Wabba ya ce wannan zanga-zanga ba na son rai ba ne, NLC na yi ne don ma’aikatan jihar Kaduna kuma ba zasu shagaltu da barazanar da gwamnan jihar yake yi wa yan kungiyar ba.

Gwamna El-Rufai yayi kurin duk wanda ya gaya wa gwamnati inda Wabba yake zai bashi na goro. Ya bayyana cewa ko shi Wabba ya kai kansa ofishin ‘Yan sanda ko kuma a kamo masa shi.

Yajin Aikin Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan asibitoci mallakar jihar Kaduna da kabda su kuskura su shiga yajin aikin da Kungiyar kwadago da fara a Kaduna.

A wata doguwar sanarwa da ya fitar ranar Talata, El-Rufai ya ce duk wacce aka samu ta shiga yajin aikin, ta sani ita ma ta yi sallama da aikinta kenan a jihar. Hatta albashin ma’aikacin na wannan watan ba za a biya shi.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa duk malamin makarantan da ya ki zuwa aiki, musamman a jami’ar jihar Kaduna, shima ya sallami kan shi kenan.

Wannan gargadi, bai tsaya ga nas nas, likitoci da malaman Jami’a ba har da ma’aikatan hukumomin gwamnatin jihar.

Gwamnati ta ce da gangar wasu ma’aikatan asibitocin jihar suka ki duba marasa lafiya da sunan wai suna yajin aiki.

Duk da cewa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnati na neman shugaban NLC Ayuba Wabba ruwa a jallo, kwatsam ku sai ga shi da dandazon yan kungiyar Kwadago sun dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

NLC ta ce za ta yi zanga-zanga har na kwana biyar a jihar Kaduna wa da hakan ya sa kusan komai ya tsaya cak a jihar.

Babu ruwa babu wuta ba, nan fetur, komai ya tsaya cak a jihar.

Gwamnan jihar Kaduna ya Nasir El-Rufai ya yi kira ha ‘Yan Kaduna su nemo masa shugaban kungiyar Kwadago Ayuba Wabba, cewa wai shi mai laifi ne.

El-Rufai ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa duk wanda ya fadi wa gwamnati inda Wabba ke boye za a bashi ladar kudi masu yawa.

Ya ce yajin aikin da Wabba ya kira a jihar Kaduna, ya saba wa doka, saboda haka gwamnati na neman sa a cafke shi, kuma duk wanda ya bada bayanan inda yake ko ya yi sanadiyyar aka kama shi za a bashi kyautar kudi mai tsoka.

Yau an shiga cikin kwana na uku a yajin aikin da ake yi a jihar Kaduna.

Sai dai kuma an samu rahoton, cewa wasu matasa sun afka wa masu zanga-zanga a daidai shataletalen Kamfani NEPA a Kaduna.