IDAN BANKIN CBN YA GAZA A NEMO ‘YAN TSIBBU DA BOKAYE: Naira ta kwarkwance, ta fara yawo tsirara a tsakiyar kasuwa

Wani kamfen da jam’iyyar APC ta buga a shafin twitter na ɗaya daga cikin mambobin ta a ranar 28 Ga Disamba, 2014, an tozarta gwamnatin Goodluck Jonathan, aka nuna cewa Naira ta kai 198 duk kowace Dalar Amurka 1.

A kamfen ɗin an nuna idan aka zaɓi APC a 2015, dala za ta koma dai da Naira 1 da sulai 7. Wato ƙasa ma da Naira 2 kenan.

Ba mamaki mai karatu ba zai fahimci wannan gagarimar matsala ba sai ya karanta yadda wani ɗan kasuwa ya yi wani bayani mai tayar da hankali a shafin sa na Facebook, a ƙarƙashin wasu taransfominin wutar lantarki da ya buga hoton su a shafin. Ga abin da ya ke cewa:

“Waɗannan taransfominin da ku ke gani, kuɗin shigo da su Najeriya a 2014, sun kai Dala 300,000. Daidai da Naira miliyan 49.8 a wancan lokacin.

“Har yanzu farashin shigo da su na nan a Dala 300,000 daga waje, bai canja ba. Amma maimakon ya tsaya daidai da Naira miliyan 49.8, yanzu haka a cikin Satumba, kuɗin daidai su ke da Naira miliyan 109.2.”

Yayin da Dala ta kai Naira 550 a ranar Litinin, ranar Talata kuma ta cilla zuwa Naira 557. Yayin da a ranar Laraba ta kai Naira 562 a kasuwar ‘yan canji.

A wannan mawuyacin hali da ake ciki, Babban Bankin Najeriya CBN wanda shi ne ya haifar da wannan jangwangwama ya yi shiru.

Wannan ragargajewar darajar Naira ta ƙara muni ne bayan CBN ya daina sayar da kuɗaɗen ƙasashen waje ga ‘yan canjin kasuwar tsaye (BDC). Tun daga ranar da aka yi sanarwar kuwa a kullum sai farashin dala ya tashi a kasuwa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta shiga shafin bayanan farashin hada-hadar ‘yan canjin Legas, wato abokiFX.com a ranar Laraba da yamma.

A ciki, wakilin mu ya ga farashin kuɗaɗen ƙasashen waje kamar haka:

Dalar Amurka 1 = N562.

Fam (€) na Birtaniya 1 = N760.

EURO 1 = N648.

Haka nan kuma a yanzu haka ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 33, yayin da a ranar Litinin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sake neman amincewar Majalisar Dattawa domin ya sake ciwo wani bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.2.

Duk wannan gurungunɗumar kuma a kullum tsadar rayuwa sai ƙara ƙamari ta ke yi, kayan abinci da kayan massrufi sai farashin su ke hauhawa. Ga kuma matsalar tsaro da ke ƙara buwayar al’ummar karkara, musamman a Arewacin Najeriya.