Hukumar NDLEA ta kama gidajen yin buredi da ke hada garin fulawa da ganyen Wiwi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta ƙama wasu gidajen da ake yin Biredi da kayan ciye ciye da garin fulawa amma suna hadawa da ganyen Wiwi.Wadannan gidaje sun hada da KNL Lounge dake hangar Lamingo da wanda ke Mining Quarters, Rantya Low Cost estate sannan da Tuscany Lounge dake hanyar Azaki Ave a cikin garin Jos.
Darektan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.
Muggan kwayoyin da hukumar ta kama sun hada kilogram 14 na Barcadin Codeine, kilogram 355.5 na Flunitrazapem, Exol-5, kilogram 30, Diazepam kilogram 2.5, Tramadol gram 370.1 da Pentazocine kilogram 1.5 a garin.
Shugaban hukumar NAFDAC dake jihar Filato Ibrahim Braji ya ce sun kama mutum biyar dake da hannu a safarar wadannan miyagun kwayoyi.
Babafemi ya ce hukumar ta kama wata budurwa mai shekaru 28 Oodo Ndidiamaka dauke da hodar ibilis gram 80.23 da methamphetamine gram 3.81 a Nsukka jihar Enugu.
Shugaban hukumar NDLEA dake jihar Enugu Abdul Abdullahi ya ce hukumar a shirye take wajen ganin ta kamo sauran mutanen dake safaran muggan kwayoyi a jihar.
Bayan haka Babafemi ya ce NAFDAC dake jihar Neja ta kama wani matashi mai shekara 24 Abel Godwin Idio da laifin safaran miyagun kwayoyi a jami’ar koyar da kimiya dake Minna.
Ya ce hukumar ta gano cewa Abel na safaran miyagun kwayoyin Arizona da loud a cikin makarantar inda yake boye miyagun kwayoyi a cikin takardu yana siyar wa dalibai a Jami’ar.
Babafemi ya ce an kama Abel a Gidan Kwano dake kusa da Jami’ar ranar 30 ga Afrilu.
Ya ce hukumar ta kara kama wasu mutane biyu Yahaya Joshua da Yahaya Audu dake safaran miyagun kwayoyi a jihar.
Babafemi ya ce an kama wadannan mutane ranar 1 ga watan Mayu a hanyar Mokwa-Jebba dauke da wiwi kilogram 32.
Shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya jinjina namijin kokarin da shugabanin hukumomi hukumar dake jihohin Neja, Enugu na kokari da suke yi domin kawo karshen safarar muggan kwayoyi a jihohin su.