Bill Gate zai saki matarsa Melinda

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Kafafen yaɗa labarai na ƙasashen duniya ciki har da VOA Hausa sun ruwaito Attajirin duniyan nan ɗan Asalun Amurka Bill da matarsa Melinda Gates sun ba da sanarwa a ranar Litinin cewa za su rabu.

Majiyarmu ta VOA ta ce Gates, wanda da shi aka ƙirƙiri kamfanin Microsoft, da matarsa, sun amince za su ci gaba da aiki tare a gidauniya mafi girma a duniya da suka kafa, wacce ake ƙira Bill & Melinda Gates Foundation.

Cikin wasu saƙonnin Twitter iri ɗaya da suka wallafa, sun ce sun amince za su kawo ƙarshen aurensu da suka kwashe shekara 27.

“Mun reni ‘ya’ya uku, mun kuma kafa gidauniya wacce ke aiki a duk faɗin duniya da zimmar ganin jama’a sun yi rayuwa cikin ƙoshin lafiya da inganci,”. A cewar sanarwar tasu.

A sanarwar suka ci gaba da cewa “Muna buƙatar sukuni da sirri daga jama’a a daidai wannan lokaci da iyalinmu ke ƙoƙarin fara wata sabuwar rayuwa.” Kamfanin Dillacin Labarai na AP