Hukumar Ƙidaya ta hori mutanen jihar Gombe su rika yi wa jariran su rajista da zaran an haife su

Hukumar kidaya NPC reshen jihar Gombe ta hori mutanen jihar da su rika yi wa ‘ya’yan su rajista da zaran an haife su.

Jami’in yi wa mutane rajista na hukumar Adedeji Adeniyi ya fadi haka da yake ganawa da manema labarai a garin Gombe a makon jiya.

Adeniyi ya ce ya yi wannan kira ne saboda yawa yawan yaran da ake haihuwa a jihar ba a musu rajista.

” Muna kira ga iyaye da su rika yi wa ‘ya’yan su rajista da hukumar kuma ya ce yi wa yara rajista kyauta.

A jihar hukumar NPC ta yi wa yara 126,674 rajista daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2021.

An yi wa wadannan yara rajista a wuraren yin rajista 77 da hukumar ta bude a jihar.

Hukumar NPC ta ce a tsakanin wannan lokaci an yi wa yara masu shekara daya 37,650 rajista inda a ciki akwai mata 20,033 da maza 17,617.

NPC ta kuma yi wa yara ‘yan ƙasa da shekara biyar 68, 396 rajista inda a ciki akwai mata 34, 394 da maza 34, 002.

Hukumar ta kuma yi wa yara ‘yan sama da shekara biyar 20, 628 a ciki akwai mata 10, 412 da 10, 216.

Adeniyi ya ce hukumar za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki domin ganin iyaye sun rika yi wa ‘ya’yan su rajista a jihar.

Ya ce yi wa yara na taimaka wa gwamnati wajen tsara kudirorin da zai amfani mutane.

Adeniyi ya ce hukumar za ta bude wuraren yin rajista a kauyuka domin karfafa gwiwowin mazauna karkara kan yi wa ‘ya’yan su rajista bayan an haife su.