‘Allah ya isa tsakanina da wanda ya kantara karyar wai zan koma PDP’ – Gwamna APC

Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata raɗeraɗin wai zai koma jam’iyyar PDP da ya baro.
Gwamnan Umahi ya yi wa wanda ya kirkiro wannan magana Allah ya isa, yana mai cewa kamar komawa baya ne bayan an riga an wuce wurin.
Bani da wannan shiri kuma ba zan koma PDP ba wanda ya kirkiro wannan magana yayi wa kan sa amma tsakanina da shi Allah ya isa.
Umahi ya gode wa Allah ganin karshen shekara da aka yi cewa hakan ya cancanci a yi wa Allah godiya matuka da jinjina masa na bamu damar ganin gangarowar wannan shekara cikin koshin lafiya.
Taron da aka yi a babban cocin Christ Embassy dake cikin fadar gwamnatin jihar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da mabiya.
Idan ba a manta ba, Gwamna Umahi na daga cikin nafarkon gwamnonin yankin Inyamirai da suka canja sheka daga PDP zuwa APC.