Hon. Tukura ya baiwa gwamnati shawara kan yadda za ta magance matsalar tsaro da gaggawa

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Zuru, Fakai, Sakaba da Danko/Wasagu daga jihar Kebbi, Hon. Kabir Ibrahim Tukura ya baiwa gwamnatin tarayya shawaran ha yoyin da za ta bi wurin shawo kan matsalar tsaro a ƙasar nan.

Ɗan majalisar wanda shine shugaban ƙungiyar matasa ƴan majalisun tarayya yana magana ne a wurin buɗe taron ranar majalisar matasa da duniya da ya gudana a babban ɗakin taron majalisar tarayya dake Abuja.
Taron ya samu halartar Sanata Bala Na’Allah, Sanata Ɗanjuma Goje, Hon. Simon Karu, Hon. Shina Peller, Hon. Lawal Umar Muda da dai sauran su.
Taken taron na wannan shekara shine ‘Rawar da majalisa za ta iya takawa wurin inganta tsaron ƙasa”.
Da yake jawabi a yayin taron, Hon. Tukura ya ce in har gwamnati na son magance matsalar tsaro to ya zama wajibi ta ƙara himma wurin riƙa kashe ma bangaren ilimi kuɗi domin samar da ingantaccen ilimi.
Ya kuma ƙara da cewa, sai gwamnati ta ƙara janyo matasa cikin harkokin shugabanci sa’annan ta ƙara ƙaimi wurin samar mu da abubuwan yi.
A yayin taron, mahalarta sun bada gudumawa da tambayoyi tare da samun amsoshi daga Sanatoci da ƴan majalisun da suka halarci taron.