Emanuel Macron ya naɗa BUA shugaban majalisar kasuwancin Faransa da Najeriya

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya naɗa attajirin ɗan kasuwar nan, Abdul Samad Isyaka Rabiu, a matsayin shugaban Majalisar Kasuwancin Faransa da Najeriya.

Majalisar mai zaman kanta ce da aka samar domin bunƙasa alaƙar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Macron ya naɗa Abdulsamad, wanda shi ne  shugaban rukunin kamfanonin BUA, a matsayin shugaban farko na majalisar a taron kasuwanci da ya gudana a Faransa.

Sabbin ƴan majalisar a Najeriya sun haɗa da Gilbert Chagoury na kamfanin Chagoury Group, Mike Adenuga mai kamfanin Glo (Globacom) da Conoil, Aliko Dangote mai kamfanin Dangote, Tony Elumelu shugaban Bankin UBA & Heirs Holdings, da Herbert Wigwe, shugaban bankin Access.

Manyan kamfanonin Faransa wadanda dake cikin majalisar sun haɗa hada da Dassault, Danone, Axens, Ponticelli da Total Energies suma mambobin majalisar ne.

Da yake jawabi a taron farko na majalisar, Rabiu ya gode wa Macron da ya nada shi kuma ya yi alkawarin amfani da majalisar don samar da kyakkyawar dama ga kasuwanci a bangarorin biyu.

Dangane da naɗin, sugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Abdulsamad Rabiu murna.

Sakon taya murnar na Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar a ranar Laraba.

Shugaban ya ce naɗin shugaban kamfanin BUA, daga buɗe majalisar kasuwanci tsakanin Faransa da Najeriyar, ya ƙara nuna ɗorewa da ci gaba da ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu wanda ke nuna kwatankwacin kawance a matakai daban-daban, da suka hada da tsaro, ilimi da kiwon lafiya.

Ya ce a baya-bayan nan Abdulsamad ya taka rawar gani a bangaren kiwon lafiya, musamman wajen yakar cutar Korona.

Buhari ya taya dukkan ‘yan ƙasuwar murna kan nasarar da suka samu a wajen taron wadda aka gudanar a birnin Paris na ƙasar Faransa.