HANA TIWITA A NAJERIYA: Za mu ƙalubalanci Gwamnatin Buhari a kotu -Inji SERAP

Kungiyar SERAP ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya ta twitter da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, haramtacce ne, kuma ƙungiyar ta ce za ta gaggauta maka gwamnatin tarayya kotu.

SERAP ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter, ko kuma ta maka ta kotu kai-tsaye.

A yau Juma’a ce Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana dakatar da twitter daga amfani a Najeriya har sai yadda hali ya yi.

Kaakin Yaɗa Labarai na Minista Lai, Segun Adeyemi ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin ministan.

Sai dai kuma jim kaɗan bayan fitar da sanarwar, SERAP a fusace ta kira dakatarwar haramtacciya, kamar yadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Olueadare ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.

“Dakatar da twitter a Najeriya tauye wa ‘yan Najeriya ‘yancin faɗar albarkacin bakin su ne da kuma toshe masu wata muhimmiyar kafar samun bayanai da aika saƙonni.

“Wannan dakatarwar wani salo ne aka yi amfani da shi na azabtar da mutane bai-ɗaya a lokaci guda. Hakan ya saba wa tsarin dokokin ƙasa-da-ƙasa.

“Saboda haka mu na kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta janye wannan dakatarwar, cikin sa’o’i 48 ko kuma mu da shi mu haɗu a kotu, saboda ya danne haƙƙin jama’a masu tarin yawa.