HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

Hukumar Alhazawa ta jihar Katsina ta bayyana cewa duk maniyyacin da shekarun sa ya zarce shekaru 65 ba zai sauka kasar Saudiyya ba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Badaru Bello-Karofi ya sanar da haka a garin Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron wayar da kan maniyyata Bello-Karofi ya ce kasar Saudiyya ta yi gargaɗin cewa kada wanda ya wuce shekaru 65 ya tafi kasar aikin haji a ban.
Hukumar ta shirya taron a cibiyoyinta dake Kankia da Dutsinma domin fadakar da maniyata kan yadda za su shirya zuwa kasar Saudiyya aikin haji.
“Kasar Saudiyya ta ce duk wadanda suka dara shekaru 65 ba za su aikin haji ba sannan yin allurar rigakafin cutar korona da gabatar da sakakamon gwajin cutar da ya nuna mutum bai kamu da cutar ba ya zama dole.
Bayan haka shugaban hukumar Suleiman Nuhu-Kuki ya jinjina kokarin da hukumar ta yi na shirin tafiya aikin hajin bana
Nuhu-Kuki ya jadaddawa maniyyata kan tsarkake kansu kafin su tafi aikin hajjin
Ya ce bana hukumar ta amince wa maniyyata da su ajiye naira miliyan 2.5 kudin tafiya.
Bana an samu tashin farashin kudin jirgi a dalilin tsadar farashin dala da aka samu
Nuhu-Kuki ya ce bana mutum 2,146 za su tashi daga jihar Katsina.