Hafsat Ganduje ta halarci saukar karatun autan ta a Landan, bayan babban ɗan ta ya kwance mata zani a kasuwa

Hafsat Ganduje, matar Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ta jibire wa gayyatar da EFCC ta yi mata, maimakon haka, ta garzaya Landan domin halartar bikin saukar karatun kammala digiri na ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta.

Hafsat ta lula Landan daidai lokacin da Hukumar EFCC ta gayyace ta domin amsa tuhumar bincike, dangane da wani ƙorafin zargin danne wasu maƙudan kuɗaɗe da ɗan ta ya yi mata.

Harƙallar dai na da nasaba ce da daƙa-daƙar filaye a Kano.

A ranar Alhamis ce EFCC ta gayyaci Hafsat, wadda a Kano hatta mijin ta Ganduje ke kiran ta da laƙabin Gwaggo.

Ɗan ta Abdul’aziz Ganduje ne ya rubuta wa EFCC takardar ƙorafin cuwa-cuwar da ya yi iƙirarin mahaifiyar sa ta yi.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwaggo mai suna Abubakar Ibrahim ne ya bayyana tafiyar ta Landan a ranar Talata.

Dama kuma a ranar Talata an riƙa watsa hotuna da bidiyo mai ɗauke da Gwamna Ganduje, Hafsat Ganduje da wasu ‘ya’yan su tare da ɗalibin da ya kammala karatun na sa Landan.

“Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Matar sa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da iyalan su, sun halarci bikin saukar karatun autan su Muhammad Abdullahi Umar Ganduje a Jami’ar Regent da ke Landan. Ya kammala digirin sa na farko, a yau Talata, 14 Ga Satumba, 2021.” Inji kakakin Gwaggo.

An dai gayyace ta domin ta halarci amsa tambayoyi a hedikwatar EFCC da ke Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, amma ba ta je ba.

Ɗan ta mai suna Abdulazeez ne ya kai ƙarar ta Hukumar EFCC, inda majiya ta ce ya fallasa yadda Gwaggo ta tsoma yatsun ta cikin dagwalon dattin ruwan harƙallar filaye a Kano, domin ta ƙara azurta kan ta.

Dama shi ma Gwamna Ganduje ya shiga tsomomuwar zargin sunƙumen miliyoyin daloli a cikin aljifan babbar rigar sa, kamar yadda wasu faya-fayen bidiyon da aka bankaɗo su ka nuna shi.

Premium Times ta ji cewa Abdulazeez Ganduje ya ce shi aka ba kuɗaɗen ya damƙa wa mahaifiyar ta sa hannu da hannu.

“Amma bayan watanni uku sai mai neman filayen ya gano cewa duk da ya biya kuɗaɗen, bai samu filayen ba, an sayar wa wasu, sai ya nemi a biya shi kuɗin sa da bayar.” Haka wata majiya ta tsegunta.

An tambayi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, wanda ya ce ba shi da masaniyar hakan ta faru.

An kira lambar Kakakin EFCC Wilson Ewujeran, amma ba a same shi ba.

Wasu na cewa EFCC za ta iya aikawa a damƙe Gwaggo matar Ganduje, tunda ita ba ta da rigar kariyar tuhuma, kamar irin wadda mijin ta Ganduje ke da ita, a matsayin sa na gwamna.