Gwamnoni na neman a ƙara farashin Man Fetur zuwa N408

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi wata zama ƙarƙashin jagorancin shugabanta gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayomi a ranar Laraba.

Ƙungiyar ta yi zaman ne a yanar gizo domin karban rahoto daga kwamitin da ta kafa kan tsaida farashin Man Fetur.

A wajen wannan taro, kwamitin ya bada shawarar a riƙa saida litar mai tsakanin N380 da N408.5.

Jaridar The Eagle ta ce kwamitin ya buƙaci gwamnati da ta cire tallafin man fetur.

Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i wanda shi ke jagirantar Kwamitin, ya ce gwamnati ta na asarar N70b-N210b a kowane wata saboda ana saida litar man fetur a kan N165 har yanzu.

Kwamitin na NGF ta bakin Gwamna Nasir El-Rufai ya bada shawarar a saida Man Fetur a kan N408.5, idan ƴan ƙwadago sun matsa, sai a bar farashin a N380.