Gwamna Ben Ayade ya fice daga PDP

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade ya sauya sheƙa daga jam’iyar PDP zuwa APC mai mulki.

Gwamna Ayade ya bayyana wannan matsayar tasa a safiyar Alhamis a wata ganawa da gwamnonin APC shida da suka ziyarce shi a gidan Gwamnatin jihar dake birnin Calabar.

Gwamnonin da suka ziyarci Ayade sun haɗa da Gwamnonin Kebbi, Imo, Yobe, Plateau, Jigawa, da Ekiti.

A ranar 5 ga watan Mayun da muke ciki Ben Ayade ya gana da abokan aikinsa Gwamnonin Jihohin Sokoto, Enugu da Delta waɗanda suka je jihar domin ɗinke baraka da ta kunno kai a jam’iyar PDP a jihar ta Cross Rivers.