Gwamnatin Tarayya za ta saya wa Kwastan motoci 46 akan biliyan N1.6bn

Majalisar zartaswa ta Tarayya (FEC) ta amince da siya wa hukumar yaƙi da fasa ƙauri ta ƙasa wato Kwastam motoci guda 46 domin ƙara inganta gudanar da aikin ta.

Ƙaramin Ministan Kuɗi da Tsare-Tsare na ƙasa, Clem Agba, ya yi wa manema labarai karin haske a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartaswa ‘FEC’ a ranar Larada da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Gwamnatin Tarayya za ta saya wa Kwastan motoci 46 akan biliyan N1.6bn
Masu garkuwa da malaman Jami’ar Abuja sun buƙaci a biya su N300m

Ministan ya ce motocin za su ƙara habaka ayyukan hukumar tare da ƙara samar da kuɗaɗen shiga.
“A yau majalisar ta amince da siyan motoci guda 46, na aiki ga Hukumar Kwastam ta Najeriya.
“Kamfanin Messrs Elizade Nigeria Limited ne aka baiwa kwangilar akan kuɗi naira biliyan 1.5 kuma wannan adadin ya hada da kashi 7.5 na harajin VAT.
“Ku tuna cewa a shekarar 2017 da 2020 ne kawai aka siya wa hukumar motoci”.
“Kuma a shekarar 2020, mun ga yawan manyan kame-kamen miyagun kaya da hukumar kwastam ta yi da kuma yadda ake samun kuɗaɗen shiga.
Ya ce kamar yadda tun a watan Agusta 2021, NCS ta cimma adadin abin da aka sa a gaba.
“Don haka, majalisar ta yi imanin cewa, idan aka samar da waɗannan ƙarin motocin, hakan zai ƙara inganta ba wai kawai aikin su ba, zai ƙara yawan kuɗaɗen shiga,” in ji shi.

Tura Wa Abokai