Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi likitoci kada su kuskura su tafi yajin aiki

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi Kungiyar Likitocin Najeriya ta NARD cewa kada su sake su fara jayin aikin gargaɗi na kwana biyar da su ce za su fara a yau Laraba.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya yi masu wannan gargaɗi a ranar Talata, a Abuja, jim kaɗan bayan ya samu wasiƙar da su ka aika masa, mai ɗauke da sanar masa cewa za su fara yajin aiki.

Cikin wata sanarwar da Minista Ngige ya fitar mai ɗauke da sa hannun Kakakin Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ƙwadago, Olajide Oshundun, ya ce yajin aikin na su haramtacce ne, kuma karya doka ne.

Makonni biyu da su ka gabata dai Minista Ngige ya ce likitocin da ke neman ƙarin albashi hauka su ke yi.

A gefe ɗaya kuma ya yi kuka da albashin da ake biyan sa.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya ce akwai rashin tunani a likitocin da ke neman a gyara masu tsarin biyan albashin CONMESS, sannan a biya su ariyas na tsarin albashi tun daga 2014.

Likitocin waɗanda ke cikin Ƙungiyar Likitocin Cikin Gida ta (NARD), sun bayar da wa’adi a ranar Asabar cewa a biya su dukkan ƙarin albashin su da kuɗaɗen ariyas, tun daga 2015.

Sannan kuma sun nemi a biya su kuɗaɗen alawus ɗin horaswa na 2023, wato MRTT.

Idan ba a biya su ba nan da makonni biyu, to za su tafi yajin aikin da ba su san ranar komawa bakin aiki ba.

Sun kuma yi tir da wani ƙudirin da ake neman amincewa da shi a majalisa, wanda ake ƙoƙarin kafa dokar da ta hana likitoci fita waje, har sai sun yi tsawon shekaru biyar su na aiki a Najeriya kafin su tsere zuwa ƙasashen waje.

Minista Ngige ya maida masu raddin cewa likitocin ba su da godiyar alherin da wannan gwamnatin ta masu.

Ya ce sun wuce makaɗi da rawa wajen neman ƙarin albashi da kuɗaɗen alawus.

‘Ni Ma Albashi Na Ya Yi Min Kaɗan, Bai Kai Naira Miliyan 1 A Wata Ba’ – Minista Ngige:

A wata tattaunawa da Ngige ya yi da gidan talabijin na Channels dangane da Ranar Ma’aikata, ya ce shi kan sa a matsayin sa na Minista albashin da ake biyan sa duk wata bai kai naira miliyan ɗaya ba.

Ngige ya ce Naira 942,000 ake biyan sa a wata. Kuma a cikin kuɗin zai fitar da albashin hadimin sa, sannan kuma ba shi da wani alawus, sai da idan ya yi wata tafiya a waje, to shi ne za a biya shi Naira “100,000, Ƙaramin Minista kuma kuɗin alawus-alawus ɗin tafiye-tafiye na sa Naira 75,000 ne.”

Makonni biyu da su ka gabata, shi ma Karamin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya bayyana cewa, “na fi samun kuɗi a sana’ar lauya fiye da abin da ya ke samu a matsayin minista.

“Kai bari ma na faɗa da babbar murya, ni fa aikin lauya da harkar dillancin gidaje ya fi min samun kuɗaɗe fiye da riƙe muƙamin minista. Ta yaya za a ce babban lauya kama ta da ya shafe shekaru 30 ina aikin lauya da harkar kadarori da shiga tsakanin masu husuma a duniya ina samun kuɗi, amma a riƙa yi min kallon wai ban isa mallakar gida a Amurka ba?, inji Keyamo cikin raddin da ya mayar wa masu surutai bayan ya watsa wani bidiyon sa a tiwita, inda aka nuno shi a gidan sa da ke Amurka ya na zaune da kayan motsa jiki, inda ya ke hutu a can.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo, ya maida wa masu sukar sa kakkausan raddi kan yadda ya mallaki gida a Amurka.

Lamarin dai ya faru ne bayan da ya watsa wani bidiyo a ranar Asabar, inda aka nuno shi ya na shaƙatawa a gidan sa da ke Amurka.

Masu suka da adawa da dama sun riƙa tambayar yadda aka yi ya mallaki gida Amurka.

Keyamo ya ce masu sukar sa ba su da ƙoshin tarbiyya da sanin ya kamata.

Ya ce ya mallaki kadarori a Amurka, ciki kuwa har da gidan da aka nuno shi a ciki ya na hutun shaƙatawa a Amurka.

Ya ce ya kwashe sama da shekaru 30 ya na neman kuɗi a aikin lauya, ba a cikin Najeriya kaɗai ba, har a ƙasashen waje.

“Kai bari ma na faɗa da babbar murya, ni fa aikin lauya da harkar dillancin gidaje ya fi min samun kuɗaɗe fiye da riƙe muƙamin minista. Ta yaya za a ce babban lauya kama ta da ya shafe shekaru 30 ina aikin lauya da harkar kadarori da shiga tsakanin masu husuma a duniya ina samun kuɗi, amma a riƙa yi min kallon wai ban isa mallakar gida a Amurka ba?, inji Keyamo cikin raddin da ya mayar wa masu surutai bayan ya watsa wani bidiyon sa a tiwita, inda aka nuno shi a gidan sa da ke Amurka ya na zaune da kayan motsa jiki, inda ya ke hutu a can.

“Tun kafin na zama minista na tara kuɗaɗen da na sayi gidaje. Ya ce kuma ya fara bayyana wa Hukumomo kadarorin sa tun ma a shekarar da aka naɗa shi mamba a Hukumar NDIC.

Ya ce kuma dukkan kadarorin sa na da rajista a Hukumar CCB.

“Kuma a cikin fam ɗin da na bayyana kadarori na, duk na rubuta asusun ajiya ta na bankunan waje, da adadin kuɗaɗen da ke cikin kowane asusun. Na yi haka a lokacin da aka naɗa ni Minista, cikin 2019.

“Kuma cikin 2021 na sai da na rubuta wa hukumomin da abin ya shafa, na ce masu ina so na kwashe kuɗi na da ke waje ajiye a asusun banki, zan sayi kadarori da kuɗaɗen, maimakon na bar su ajiye a banki.”

Ya ce mutane da dama sun raina shi, gani su ke yi bai cancanci mallakar kadarorin ba.

Matsalar Ƙarancin Likitoci A Najeriya:

Cikin watan Nuwamba, 2022, Kungiyar Likitocin Najeriya ta ce likitoci 24,000 ne kaɗai a Najeriya, sauran sun gudu Ingila, Saudiyya da Qatar.

A labarin wanda PREMIUM TIMES Haisa ta buga, Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Rowland Uche, ya bayyana cewa a yanzu likitocin da su ka rage a Najeriya ba su wuce 24,000 ba, duk kuwa da cewa al’ummar ƙasar ta kai yawan mutum miliyan 200.

Ya ce hakan na nuni da cewa duk likita 1 ya na kula da mutum 10,000 kenan.

“A kudancin ƙasar nan likita ɗaya ne ke kula da mutum 30,000. Amma a Arewa akwai ma inda likita ɗaya ne tilo a cikin mutum 45.

“Abin takaici a yankunan karkara wasu sai sun yi tafiyar sama da kilomita 30 kafin su samu ganin likita.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta ce kamata ya yi a ce akwai gamayyar likitoci, nas-nas da unguwar zoma 23 a duk mutum 10,000.

Haka kuma Rowland ya Yi ƙarin bayani dangane da yadda ƙwararrun likitocin Najeriya fiye da 5,000 su ka yi hijira zuwa Ingila.

An tabbatar da cewa fiye da ƙwararrun likitoci ‘yan Najeriya 5,000 ne su ka tsallake zuwa Ingila a cikin shekaru takwas.

Tabbacin adadin waɗannan alƙaluma ya fito daga bakin Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Uche Rowland, yayin da ya ke jawabi wurin wani taron tattauna ƙarancin likitoci a Najeriya da kuma dalilin yawan ficewar su zuwa ƙasashe, musamman Ingila.

An shirya taron ne a Abuja ranar Laraba, a ƙarƙashin ƙungiyar dRPC.

Najeriya na fama da ƙarancin likitoci ta yadda aƙalla an yi ƙiyasi da kirdadon cewa likita 1 ne ke duba mutum 5,000, saɓanin ƙa’idar da Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindiya cewa kada likita 1 ya zarce duba mutum 600 kacal.

Yadda Likitocin Najeriya Ke Tururuwar Zuwa Ingila:

“Cikin 2015 likitoci 233 ne su ka koma Ingila su na aiki. A cikin 2016 kuma likitoci 276 ne. Sai kuma cikin 2017 likitoci 475 su ka yi ƙaura zuwa Ingila su na aiki.

“Cikin 2018 kuwa an tabbatar da tafiyar likitoci 856, sai kuma cikin 2019 har likitoci 1,347 su ka tafi Ingila yin aiki a can.

“Cikin 2020 wasu likitoci 833 su bi hanya zuwa Ingila, sai kuma wasu 932 a cikin 2021.” Haka Rowland ya tabbatar.

Fargabar Ƙwararar Likitocin Najeriya Zuwa Ingila A 2022:

Rowland ya kuma tabbatar da cewa a cikin watanni shida na farkon 2022, ƙwararrun likitocin da aka bai wa horon aikin likita a Najeriya har su 737 ne su ka fice zuwa Ingila.

Ya ce lamarin abin tsoro ne, domin hakan ya nuna cewa adadin yawan waɗanda su ka koma Ingila cikin 2022 zai zarce na kowace shekara, idan aka haɗa da lissafin waɗanda su ka fita daga watan Yuni zuwa Disamba 2022, domin ba a lissafa da su daga ɗin ba.

Rowland ya ce ƙasar Indiya ce ta fi yawan likitoci baƙi a Ingila, sai Pakistan, sai kuma Najeriya wadda ita ce ta uku.

An tabbatar da cewa akwai ƙwararrun likitoci ‘yan a Ingila za su kai 9,976.

Jami’an Lafiya 13,609 Sun Shiga Ingila Daga Najeriya Cikin 2022 -Hukumar
Shige-da-ficen Ingila:

Hukumar Kula da Shigar Baƙi Cikin Ingila ta fitar da rahoton cewa aƙalla adadin jami’an lafiya 13,609 aka bai wa lasisin shiga su yi aiki cikin Ingila a cikin 2023.

Hukumar ta ce an bai wa ‘yan Indiya har mutum 43,966 wannan damar.

Dalilin Ficewar Likitocin Najeriya Zuwa Ingila:

Rowland ya ce daga cikin dalilan ficewar akwai yadda gwamnati ba ta ɗaukar batun kiwon lafiya da muhimmanci.

“Kasafin bara Gwamnatin Tarayya ta ware wa fannin lafiya ƙasa da kashi 5% cikin 100% na kasafin kuɗi. Sannan kuma akwai matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke yawan yin garkuwa da likitoci, ‘yan ta’adda kuma na yawan kashe wasu.”