Gwamnatin Najeriya Za Ta Rufe Kamfanonin Ba Da Rancen Kudi Da Suka Saba Kai’da

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Najeriya wato FCCPC ta bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya ta kafa domin magance tauye hakkin mabukata da rashin adalci a masana’antar ba da rancen kudi za ta rufe sana’o’in masu ba da rance ba bisa ka’ida ba.