Gwamnatin Edo ta soke kwangilar wata hanyar da ta gano badaƙala a kanta

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnatin jihar Edo ta ɗauki nauyin gina titin mazabar tarayya ta Lawani Crescent a ƙaramar hukumar Akoko-Edo ta jihar.

Hakan ya biyo bayan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda ya fallasa yadda aka yi aiki ba bisa inganci ba, inda nan take gwamnatin ta gudanar da binciken aikin kuma ta ce ta tabbatar da rashin ingancin sa kanar yadda ya bayyana a bidiyon.

Gwamnatin a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ingancin hanyar bai kai kwatankwancin aiyukan hanya da take shimfiɗawa a faɗin jihar ta Edo ba.

Ta jinjina wa matashin da ya yaɗa bidiyon tare da yin ƙira da al’ummar jihar da su zuba ido akan kayaki da aikin gwamnati a yankunan su.

“Dole ne a kama ɗan kwangilar da ke gudanar da aikin titin Lawani Crescent bisa almundahana da ya aikata domin miƙashi ga hukumar ICPC da EFCC don ba mu damar gano ainihin abin da ya faru”. A cewar gwamnatin.

A cewar gwamnatin, an soke kwangilar aikin.

An bayyana cewa Majalisar tarayya ta ware naira miliyan N360 don ayyuka a mazabar Akoko-Edo a wannan shekarar, gwamnatin tana mai cewa za ta bincika domin sanin ainihin kuɗin da aka baiwa ɗan kwangilan.