Gwamnatin Buhari za ta murkushe ‘yan bindiga a kasar nan – APC

A ranar Litini ne Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta dada jaddawa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta murkushe ‘yan bindigan da suka addabi mutane a sassan kasar nan nan bada dadewa ba.
Sakataren kwamitin jam’iyyar na CECPC sanata John Akpanudoedehe ya sanar da haka a wani takarda da aka rabawa manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Akpanudoedehe ya ce jami’iyyar APC ba ta ji dadin yadda yadda ‘yan bindiga ke kisan mutane a jihar Zamfara da sauran jihohin Arewacin kasar nan.
Ya ce a yanzu haka gwamnati ta zage damtse wajen ganin ta samar wa jami’an tsaro kayan aiki domin inganta aiyukkan samar da tsaro a fadin kasar nan.
“Gwamnati ta dibi karin dakaru sannan ta horas da su da sauran jami’an tsaro ta kuma karo kayan aiki domin inganta ayyukan samar da tsaro a kasar nan.
Akpanudoedehe ya yabawa namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen ayyukan samar da tsaro a jihohin da rashin tsaro ya yi tsanin a kasar nan.
Ya yi wa gwamnatin jihar Zamfara da mutanen jihar ta’aziyyar rashin da aka yi na daruruwan mutane a dalilin hare-haren ‘yan bindiga.
Akpanudoedehe ya yi kira ga mutane su rika sanar da jami’an tsaro ayyukan yan bindiga a yankunan su.