Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga biyar a karamar hukumar Giwa

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi galaba akan wasu ‘yan bindiga inda suka kashe akalla biyar cikin su a Kwanan Bataro dake karamar hukumar Giwa.
Aruwan ya fadi haka a wata takarda da aka rabawa manema labarai yana mai cewa rundunar sojin Najeriya ne ta sanar wa haka wa gwamnati wannan nasara da ta yi a wannan gari.
Ya ce jami’an tsaron sun fatattaki ‘yan bindigan ne bayan sun samu bayanai na siri game da maharan a garin Fatika.
“Nan da nan jami’an tsaro suka fantsama cikin daji inda suka cimma ‘yan bindigan a garin Marke da Ruheya.
‘Jami’an tsaron sun cimma maharan a Kwanan Bataro inda suka yi musayan wuta da su har jami’an tsaron suka kashe mutum biyar daga cikinsu.
Aruwan ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya yabawa wa namiji kokarin da jami’an tsaron suka yi sannan ya hore su da su kara himma wajen kare rayukan mutane da dukiyoyi a jihar.
Idan ba manta ba a ranar 19 ga Disamba 2021 Aruwan ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum sama da 20 a karamar hukumar Giwa.
Ya ce ‘yan bindigan sun Kuma Kona gidajen mutane tare da motoci da kayan abinci.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Katsina, Sokoto, Zamfara da Neja na daga cikin jihohin da ‘yan bindiga suka adaba a Arewacin kasar nan.