Gwamnan Osun ya tilasta wa ma’aikatan jihar zuwa aiki sanye da ankon gyauton ‘adire’

Gwamna Gboyega Oyetola na Jihar Osun ya umarci dukkan ma’aikatan jihar su ɗinka anko (uniform) wanda za su riƙa zuwa aiki sanye da shi a kowace ranar Alhamis.

Gwamna ya ce kowane namiji da kowace mace za ta ɗinka gyauton ‘Adire’ su riƙa zuwa ofis sanye da shi, domin a bunƙasa al’adu da ɗabi’un mutanen jihar Osun.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, Ismail Omipidan ne ya bayyana haka, cikin wata takardar sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES.

Ya ce an ware kowace ranar Laraba ta zama ranar sanya tufafin Adire.

Ya ce tufafin Adire al’adar mutanen Osun ce. “Ashe ba banza ba ake yi wa Osogbo babban birnin Jihar Osun kirarin ‘Osogbo garin masu rini.’

Ya ce dama tun farkon hawan sa mulki ya bayyana cewa zai bijiro hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin jihar da kuma samar da aikin yi ga matasa sai kuma haɓɓaka samar da wadataccen abinci.

“Daga ranar 27 Ga Agusta 2021 kowane cikin ma’aikataci zai riƙa zuwa wurin aiki sanye da suturar da aka ɗinka da gyauton adire.”