Gwamna Inuwa na Gombe ya kadamar da shirin Inshorar lafiya ga yan jihar

Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya kaddamar da shirin inshorar lafiya ga yan jihar mai suna ‘GoHealth’.

Taron kaddamar da inshorar ya gudana a fadar gwamnati ranar Alhamis.

Yahaya ya ce gwamnati ta kafa sabuwar hukumar da za ta tabbatar shirin ya yi aiki yadda ya kamata a jihar.

“Idan ba a manta ba inganta fannin kiwon lafiya na daya daga cikin alkawarun da muka dauka a lokacin Kamfen.

“Fannin kiwon lafiyar Jihar Gombe ya tabbarbare wanda hakan ya samo asali tun daga gwamnatocin baya da suka mi maida hankali a kai.

Yahaya ya ce gwamnatin sa za ta maida hankali wajen ganin ta kawar da matsalolin da ake fama da su a fannin lafiya na jihar.

rashin samun lafiya ta gari a jihar.

Ya ce gwamnati tare da hadin guiwar babban bankin duniya ta gyara akalla cibiyar kiwon lafiya daya a kowace mazaba a jihar.

“An zuba kwararrun ma’aikata da kayan aiki na zamani domin ganin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na aiki a kowani lokaci.

Yahaya ya ce gwamnati ta kuma gyara duk manyan asibitocin dake jihar.

“Gwamnati ta kuma inganta makarantun koyar da ma’aikatan jinyar da unguwar zoma sannan ta gina gidajen zaman likitoci masu koyan aiki.

Bayan haka shugaban hukumar GoHealth Mohammed Isa-Umar ya jinjina namijin kokarin da gwamna Inuwa ya yi na kafa tsarin inshora lafiya a jihar.

Isa-Umar ya ce bayan watanni shida da kafa shirin mutum 25,000 da Suka hada da talakawa da ma’aikatan gwamnati sun yi rajista da tsarin.