GHALI YA BUƊE WUTA: ‘Mafi lalacewar cikin mu aka damƙa wa shugabancin mu’

Tsohon Kakakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na’Abba, ya bayyana cewa babu shugabanci a Najeriya.

Ghali na kuka ne a kan yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a ƙasar nan, tare da cewa talakawa na ɗanɗana kuɗar sakacin da gwamnati ta yi ana ta tashe-tashen hankula.

Kalaman Ghali wani shavube ne kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa tsayar da kashe-kashen da ke faruwa a faɗin ƙasar nan.

“Mafi lalacewa a cikin mu ne aka ɗauki amanar jagorancin al’ummar ƙasar nan aka damƙa a hannun sa.”

Ya yi waɗannan kakkausan kalaman a wani taron da ya haɗa ƙabilun Najeriya daban-daban a Abuja, a ranar Litinin.

Cikin mahalarta taron har da Ayo Adebanjo na Afenifere, Chukwuemeka Ezeife na Ohaneze-Ndigbo da sauran su.

Ghali ya yi kalaman ne a lokacin da Buhari ya cika shekaru shida a kan mulki, ba tare da magance matsalar tsaro da ya rika kamfen zai magance ba idan ya hau mulki.

Kawar da matsalar tsaro na daga cikin manyan alkawuran da Buhari ya dauka tun kafin ya hau mulki.

Yan Najeriya musamman yan Arewa sun yi goguwar Buhari ne a 2015 domin ya magance matsalar tsaro da yankin ke fama da shi a wancan lokaci wanda ita ce matsalar hare-haren Boko Haram.

Sai dai kuma shekaru shida bayan haka, maimakon a samu sauki, matsalar tsaro tsanani ya kara yi musamman yanzu kuma a yankin Arewa Maso Yamm da Kudancin Najeria.