GA ƘOSHI GA KWANAN YUNWA: Manoman rani a Katsina sun koka saboda gwamnati ta datse masu ruwan Ajiwa Dam ba sanarwa

Yayin da manoman rani a ke Ajiwa da ƙauyukan kewaye ke murnar cewa sun fara dashe da shukar kayan lambu cikin sa’a, yanzu dai murna ta koma ciki, domin Gwamnatin Jihar Katsina ta datse ruwan Madatsar Ruwan Ajiwa.

Datse ruwan da aka yi ya kawo matsala ga manoma sama da 300 a yankin, waɗanda kayan noman su ke fuskantar barazanar lalacewa da bushewa, saboda ƙarancin ruwa.

Wakilin Premium Times ya je har Ajiwa Dam, inda ya samu manoma a cikin halin damuwar tare masu ruwan dam ɗin Ajiwa da gwamnatin Katsina ta yi.

Sannan kuma ta samu da yawa daga cikin su na haƙilon gina rijiyoyin da za su riƙa samun ruwa, domin su riƙa zuba wa shuke-shuken da su ka yi a cikin gonakin su.

Wani mai suna Usman Hassan mutumin ƙauyen Gangarawa, shaida wa wakilin mu ya yi cewa idan bai sa ƙarfi ya gina rijiya don ya samu ruwa ba, to asara zai yi baki ɗaya.

Ya ce gwamnati ta yi watsi da su, babu taimako. Sannan kuma an datse masu ruwa ba tare da an sanar da su ko an ba su wa’adin kimtsawa don su nemi mafita ba.

Usman Hassan ya ce ya na noma latas, albasa da yaki.

Wakilin mu ya gano cewa gaba ɗayan manoman yankin fiye da 300 su na fara da ƙarancin ruwa.

Rabon su da ruwa tun da Gwamnatin Jihar Katsina ta kulle ruwan ba ya isa cikin gonakin su.

Lawal Umar ya shaida wa wakilin mu cewa a shekarun baya ya yi noma kuma ya samu albarkar noma. “Amma yanzu a gaskiya baƙar wahala kawai mu ke sha a wurin noman a Ajiwa. Lawal Usman ya na noma tumatir, tattasai. To yanzu an datse mana ruwa.”

Ya ce sun sha yin kuka ga gwamnati, shiru. Amma manajan Dam ɗin Ajiwa ya shaida masu cewa gara kawai su kai kukan su wurin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina. Shi kaɗai ne zai iya share masu kukan su.

Sai dai kuma wakilin mu ya tuntuɓi Kakakin Ma’aikatar Ruwa ta Katsina, Bashir Kurfi ya shaida masa cewa an kulle ruwan ne don a yi gyara kuma a ƙara faɗaɗa madatsar ruwan.

Ya ce kamfanin CCECC aka ba kwangilar aikin a kan kuɗi naira biliyan 3.309.

Bashir Kurfi ya ce ana kyautata zaton za a kammala aikin cikin watanni 18.