DUBU TA CIKA: Ni na sace mahaifina, na karɓi naira miliya 2.5 kuɗin fansa – Wani matashi

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta sanar cewa ta kama wani saurayi da ake zargin shine ya sace mahaifin sa, ya kuma karbi kuɗin fan sa har naira miliyan 2.5.
Kakakin rundunar Ajayi Okasanmi, ya ce wannan matashi ya sace mahaifin na sa ne tare da haɗin bakin wasu mutum biyu da yanzu haka ake neman su.
” Da kan sa ya faɗi cewa shine ya sace mahaifinsa kuma ya karbi kuɗin fansa har naira miliyan 2.5. sai dai kuma rundunar na ci gab da bincike da kuma farautar sauran mutum biyu da suka haɗa baki da shi suka aikata wannan mummunar abi.