Dole Ƙasashen Kudancin Sahara su tashi su hana sabuwar masifaffiyar korona jijjiga su

Bankin Bada Ramce na Duniya (IMF), ya bayyana cewa hanya mafi sauki da kuma wahala da ita ce kaɗai Ƙasashen Kudancin Sahara za su bi domin hana sabuwar korona mai suna Delta ɓarkewa a yankin su, ita su hanzarta aikin yi wa jama’a ba adadi allurar rigakafin korona kawai.

Shugabar Bankin IMF Kristalina Georgieva ta ce ƙasahen Kudancin Sahara na fuskantar ɓarkewar sabuwar korona mai suna ‘Delta, wadda ta fi korona biyu da aka yi baya saurin lahanta mutane da kashe su.

Yawan masu kamuwa da cutar yanzu a Kudancin Sahara cikin kwanakin nan, ya zarce yawan sauran yankunan ƙasashen duniya, yawan kamuwar da ake yi da wannan sabuwar korona mai suna Delta, ya zarce irin yadda aka riƙa kamuwa da sauran nau’uksn korona biyu da aka yi a baya, tun farkon fuskantar korona cikin Janairu 2020.

Jami’an IMF biyu sun ce “wanann sabuwar korona za ta iya zarce yawan waɗanda su ka kamu da cutar a baya. Saboda a wasu ƙasashen yawan masu kamuwar da cutar a yanzu.

An dai gano sabon samfurin ‘Delta’ wadda tuni aka ruwaito wani rahoton binciken da ke nuna cewa kashi 60% na da yiwuwar kamuwa da cutar, tare da saurin watsa ta.

Zuwa yanzu dai ƙasashe 14 na cikin Kudancin Sahara sun tabbatar da fantsamar cutar korona ɗin samfurin ‘Delta’ a yankunan su.

Koronar farko dai ba ta shafi ƙasashen Kudancin Sahara na. Sai ta biyu wadda ta bayyana bayan watanni shida da ɓullar ta farko.

A yanzu kuma yankin ya na fuskantar korona kashi na uku mai suna Delta.

Wata matsala da ƙasashen yankin Kudancin Sahara ke fuskanta, har yanzu yankin bai taɓuka abin yabo ba wajen yawan jama’ar da aka yi wa rigakafin korona.

Afrika dai ba a yi wa mutane da yawa rigakafin korona b.