An kara wa’adin hada layin waya da lambar katin zama dan kasa zuwa 26 ga Yuli

A karo na shida gwamnatin tarayya ta kara wa’adin ranar rufe rajistar hada layin waya da lambar katin shaidar zama dan kasa zuwa ranar 26 Yuli.

Kakakin Yada Labarai na Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, Ikechukwu Ayinde da Kakakin Yada Labarai na Hukumar Samar da Katin Dan Kasa, NIMC, Kayode Adegoke su ka sanar da haka ranar Litini.

Gwamnatin Tarayya ta yi karin ne domin masu ruwa da tsaki a fannin sun yi kira da a fadada yin rajistan hada layin waya da lambar katin shaidar zama dan kasa ganin cewa an kara yawan wuraren yin rajistan a kasar nan.

Daga ranar 28 ga Yuni an bude wuraren yin rajistan 5,410 a kasar nan.

Kara yawan wuraren yin rajistan da aka yi zai taimaka wajen rage yawan cinkoson da ake samu a wuraren yin rajista.

“A watan Disembar 2020 wuraren yin rajistan layin waya da katin dan kasa guda 800 ne kadai ake da su a kasar nan.

Zuwa yanzu an bude wuraren yin rajista miliyan 57.3 a kasar nan sannan ana hada layin waya uku zuwa hudu da katin dan kasa guda daya.

Idan ba a manta ba a karo na biyar, gwamnatin tarayya ta kara wa’adin ranar rufe rajistar hada layin waya da lambar katin shaidar zama dan kasa zuwa ranar 30 Ga Yuni.

A lokacin ministan Sadarwa Isa Pantami ne ya sanar da karin na makonni takwas din.

Pantami ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi karin ne domin ‘yan kasar nan da mazauna kasar su samu damar mallakar lambar katin shaidar NIN.