Dattijo Bashir Tofa ya rasu

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 1993, a ƙarƙashin jam’iyyar NRC, Bashir Tofa ya rasu.

Kachallan Kano, Magaji Galadima ne ya bayyana sanarwar rasuwar sa a safiyar Litinin, a shafin sa na Facebook da wasu shafukan sada zumunta na WhatsApp.

“Inna Lillahi Wa Innaa Ilaihir Raji’un. Allah ya yi wa Alhaji Bashir Tofa rasuwa. Allah Ubangiji ya jiƙan sa ya gafarta masa, ya sa aljanna ce makomar sa. Allah ya kyauta bayan sa, ya ba iyalin sa da mu duka haƙurin jure wannan babban rashi. Allahu Akbar.”

Tofa ya rasu safiyar Litinin bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya rasu ya na da shekaru 74 a duniya.

An haife shi a cikin watan Yuni, 1947, a Kano. Bayan kammala firamare da sakandare, Bashir Tofa ya yi karatu a City of London College, tsakanin 1970 zuwa 1973.

Ya fara siyasa a 1976, lokacin da ya zama kansila a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa.

Ya yi Sakataren NPN na jihar Kano a lokacin Jamhuriya ta Biyu. Daga nan kuma ya zama Sakataren Kuɗi na NPN na Ƙasa.

Bashir Tofa mamba ne na Kwatimin Shirin Bunƙasa Noma a zamanin mulkin marigayi Shehu Shagari, wato Green Revolution National Committee.

Ya shiga jam’iyyar NRC cikin 1990, kuma ya zama ɗan takarar ta na shugaban ƙasa a zaɓen 1993, inda marigayi MKO Abiola na SDP ya kayar da shi.

Bashir Tofa ya lashe zaɓen fidda gwanin NRC bayan ya kayar da Pere Ajunwa, John Nwodo da Ɗalhatu Sarki Tafida.

Hamshaƙin ɗan kasuwa ne, kuma babban attajiri. Tofa mawallafi ne, marubuci ne.

Allah ya gafarta masa.