Dan takara zai iya lashe zabe a kasar Gambiya ko bai sami mafi yawan kuri’u ba? – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya fadi cewa dan takara na iya lashe zabe a Gambiya ko da kuwa dan takaran ba shi da rinjayen kuri’u

Wani mai amfani da shafin tiwita ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa baya bukatar kuri’a mafi yawa kafin ya lashe zabe.

“ Kun san cewa mutun na iya lashe zabe a Gambia ko da mafi yawan al’umma ba su zabe shi ba? Ya kamata a daina amfani da wannan dokar rinjaye gudan. Ba shi da kan gado gaskiya,” ya rubuta.

Wannan zargin ya janyo martanoni sosai, da damansu tambayoyi inda jama’a ke so su san yadda hakan zai yiwu, wasu kuma suna so ya kara fadada musu batun su ji karin bayani dan wanda ya yi bas u fahimci abin da yake nufi da kyau ba.

“Misali, daga mutane dubu dari taran da suka yi rajista, idan Jam’iyya A ta sami kuri’u 400 yayin da sauran Jam’iyyu biyar din suka raba kuri’u dubu biyar din da suka rage, jam’iyya A ta lashe zaben ke nan duk da cewa ba ta sami kuri’u mafi rinjaye a zaben ba,” in ji mai zargin

Tantancewa

Da farko dai, dole a yi la’akari da cewa, bisa tanadin kundin tsarin mulkin Gambia, babi na biyar sashe na 39(1) da dokar zabe, sura 3:01, wadanda suka yi rajistan zabe, ba kasar baki day aba ne suka cancanci jefa kuri’a a zaben shugaban kasa.

Kuri’u nawa dan takara ke bukata dan ya zama shugaban kasar Gambia

Sashe na 81 na dokar zaben Gambia, sura 3:01, doka mai lamba 78 na 1996, ya bayyana cewa dan takaran da ya fi yawan kuri’u shi ne zai zama shugaban kasa.

“Hukumar zabe za ta bayyana sakamakon da zarar ta karbi sakamakon sa’annan ta bayyana wanda ya ci ba tare da bata lokaci ba, ko kuma idan akwai jerin sunayen ‘yan takaran sai ta bayyana wanda ya sami mafi yawan juri’un wanda ya zo daidai da sashe 79 na kundin tsarin mulkin.”

Mene ne wannan tsarin na mafi rinjaye dayan?

Tsarin mafi rinjaye daya tsarin zabe ne wanda ya barin dan takarar da ya sami mafi yawan kuri’u ya zama wanda ya lashe zabe. Wanda ya lashe zabe ba sai ya sami mafi yawan kuri’un da aka kada ba, ko kuma ya kai wani mizanin da aka kayyade ba, illa dai kawai, da zarar ya wuce sauran wadanda ya ke takara da su da yawan kuri’u shi ke nan ya lashe zaben. Wannan tsari ne da ake amfani da shi a kasashe irin su Malawai. Babban abun da tsarin ya tanada shi ne kawai dan takara daya ya tsere ma sauran a yawan kuri’u shi ke nan ya lashe zabe.

Yadda hakan ya faru a zaben 2016 na Gambia

A watan Disemban 2016 ‘yan Gambia sun je su jefa kuri’a a zaben da ya tuntsurar da mulkin kama karyan tsohon shugaba Yayah Jammeh, wanda ya shafe shekaru gomai. Wannan sai ya gyara hanyar sauyin mulki na dimokiradiyyar da ya kawo shugaban adawa Adama Barrow kan mulki a karkashin jam’iyyar United Democratic Party (UDP). Shugaba Adama Barrow ya sami kuri’u 227,708 a yayin da abokin hamayya Jammeh ya sami 208,847 sa’anan dan takara na uku Mama Kandeh ya sami 89,769 na jimilar kuri’un da aka kada, kamar yadda aka gani a sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana. Bacin cewa Adama Barrowya sami kashi 43 ne kadai na jimilar kuri’un da aka tara, ya lashe zaben ne saboda ya sami sa’a fiye da abokan hammayar ta su.

A karshe

Tsarin simple majority ko kuma mai mafi rinjaye daya ya na baiwa dan takarar da ya fi yawan kuri’u kasancewa zakara. Dan haka gaskiya ne mutun na iya lashe zabe a Gambia ba tare da ma mafi yawan al’umma ta zabe shi ba.