Dalilin da ya sa ma’aikatar Ilimi ta hana daukar yara ‘yan kasa da shekara 12 a makarantun ‘Unity School’

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa daga yanzu ba za a rika daukar yara ‘yan kasa da shekara 12 a makarantun sakandare na ‘Unity Colleges’ saboda a doka basu kai su shiga makarantar Sakandare ba.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi Andrew Adejoh ya sanar da haka a cikin makon jiya yayin da ake sa Ido a jarabawar shiga makarantun sakandare mallakin gwamnatin tarayya da aka fi sanin su da makarantun Unity.
Adejoh ya ce gwamnati a shirye take domin ganin an kiyaye wannan doka domin yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalolin da fannin ilimi ke fama da su a kasar nan.
“ Mu iyaye da kan mu muke karya wannan doka hanyar tura yara kanana da shekarun su bai kai ba suna rubuta jarabawar shiga makarantun sakandare.
“ Na ga yara da basu wuci shekara 10 ba inda uku daga cikinsu na da shekaru 9 sun shiga makarantar sakandare.
Duk shekara hukumar NECO ce take shirya jarabawar shiga makarantun sakandare na Unity Colleges.
Rajistaran NECO Dantani Wushishi ya ce bana dalibai 72,821 ne suka rubuta jarabawar inda jihar Legas da Babban Birnin Tarayya Abuja ne suka fi yawan dalibai a kasar.
Wushishi ya ce jihar Kebbi ita ce ta fi karancin dalibai inda a jihar dalibai 115 ne suka rubuta jarabawar.
Ya ce bana an kara samu dalibai mata da suka fi maza yawa mata 38,000, maza 34,000.