DA DUMI-DUMI: Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda 7 a wani kwanton bauna a Zamfara

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Wasu ƴan bindiga sun kashe ‘yan sanda aƙalla bakwai a wani kwanton bauna da suka kai a kusa da kauyen Zonai da ke gundumar Magami a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Daily Trusta ta ruwaito mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce, ƴan sandan na dawowa ne daga bakin aiki, a ranar Litinin, a wani shingen bincike da ke kusa da kauyen Zonai da ke kan titin Gusau-Magami-Dansadau, a lokacin da ‘yan bindigan suka buɗe wuta kan motar da ke dauke da jami’an tsaron.

  • Facebook

    Twitter

Labarin bayaMasu garkuwa sun sace ma’aikatan Ƙaramar hukumar Zaria mata 13

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.