Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishiniyar Muhalli ta jihar Gombe, Hussaina Ɗanjuma Goje ta yi murabus

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Ƴar tsohon Gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar jihar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje, wato Dr. Hussaina Ɗanjuma Goje ta ajiye muƙaminta.

Dr. Hussaina, wadda ta yi murabus daga kujerarta ta Kwamishiniyar Muhalli da Gandun Daji, ta sanar da hakan ne a wani gajeren jawabi da ta yi na Bidiyo ga kafafen yaɗa labarai a birnin Gombe, fadar jihar.

  • Facebook

    Twitter

Labarin bayaAn kashe mutum biyar a hatsaniyar siyasa a Gombe

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.