DA ƊUMI-ƊUMI: An kai wa Limamin Haramin Makka hari

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Da Ɗumi Ɗuminsa

Wani mutum yayi yunƙurin kaiwa Limamin Masallacin Ka’aba dake birnin Makkah hari a yau Juma’a.

Lamarim ya faru a daidai lokacin da Limamin ke tsaka da gudanar da Huɗubar Juma’ar yau, inda kawai aka ga mutum ya taso a guje ɗauke da makami da ya fito da shi daga jikinsa ya nufi Mimbarin da Lilamin yake.

Sheikh Bandar Baleelah ne ya jagoranci Sallar Juma’a ta wannan makon.

Tuni jami’an tsaro suka yi gaggawar kama mutumin tare da yin waje da shi.