Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun sace wani Sanata

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata xaton masu garukuwa da mutane ne sun yi garkuwa da Sanata Dickson Imasogie,  mai wakiltar mazabar Edo ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Daily Trust ta ruwaiti an sace ɗan majalisan ne da safiyar Litinin, inda ƴan bindigan suka tare shi a kan hanyarsa ta zuwa gona a kan titin Agbor a Jihar tare da direbansa da wani mutum.

Sanatan wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani cikakken bayani da aka samu a hukumance dangane da sace shin.

An wallafa wannan Labari September 13, 2021 3:42 PM