Da Ɗumi Ɗumi: Ƴan bindiga sun kashe Kwamishina a jihar Kogi

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni dake fitowa daga jihar Kogi sun bayyana cewa ƴan bindiga sun harbe Kwamiahinan Fansho na jihar Kogi Solomon Adebayo har lahira.

Majiyar Hausa Daily Times ta News Daily24 ta ruwaito lamarin ya faru a yammacin Asabar a kan hanyar Kwamishinan zuwa ƙaramar hukumar Kabba ta jihar daga birnin Ilorin na jihar Kwara.

Ƴan bindigar sun jikkata Direban kwamishinan tare da tafiya da duk kayakin da suka samu a cikin motar. Kamar yadda majiyar ta ruwaito.

Solomon Adebayo dai Kwamishinan ne da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya naɗa domin kula da harkokin Fansho a jihar.