Aisha Matawalle na son mata su haɗa kai don kawo karshen wariya da ake nuna musu a ma’aikatun gwamnati

Yayin da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana shirye-shiryen taimaka wa ma’aikata wajen yaƙi da talauci, Uwargidan gwamnan Hajiya Aisha Bello Matawalle ta buƙaci matan Zamfara da su jajirce wajen yaƙi da cin zarafin mata a ma’aikatun gwamnati.

Uwargidan gwamnan wacce ke jawabi a wurin taron ranar ma’aikata ta bana, ta ce cin zarafin mata matsala ce mai girma cikin al’umma da ke buƙatar kulawar mata, musamman a ma’aikatun gwamnati don ‘yantar da ‘yan uwansu mata daga wariyar da suke fuskanta daga takwarorinsu maza.Hajiya Aisha wacce ta kasance abin koyi a yaƙi da cin zarafin mata a Arewacin Najeriya, ta ce “mata a ma’aikatun gwamnati suna da rawar takawa wajen yaƙi da wariyar da suke fuskanta a hannun maza a ma’aikatun gwamnati.
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ce har sai lokacin da mata masu aikin gwamnati suka haɗa kai waje guda don yaƙi da ra’ayi guda wajen nuna wariyar mata, in ba haka ba matan Najeriya musamman a Arewacin Najeriya za su fuskanci matsala wajen samun manyan mukamai a cikin ma’aikatun gwamnati.Ta buƙaci Gwamna Bello Matawalle da ya ƙara ƙaimi a ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi na sanya ƙarin mata cikin ayyukan jihar.
Aisha Matwalle ta yaba da ƙoƙarin maigidanta na ƙarbar ƙarin mata a gwamnatinsa tare da naɗa wasu mata a mukamai daban-daban a ma’aikatun gwamnati.
Ta buƙaci magidanta da su ba matansu masu da suka yi karatu damar yin aiki a ma’aikatun gwamnati, domin bayar da tasu gudummawar a bangaren ci gaban jihar Zamfara.
Har wayau Uwargidan gwamnan ta buƙaci Sarakunan gargajiya da malaman addinin Musulunci da su taimaka wajen wayar da kan mata da kuma wayar da kan mazajen su a koda yaushe don shiga cikin ayyuka da abubuwan da suka dace don inganta jin daɗin rayuwar mata a jihar.