Cutar kwalara ta ɓarke a sansanin ‘tubabbun ‘yan Boko Haram’, har ta kashe biyu, wasu na kwance asibiti

Aƙalla mutum biyu cutar kwalara ta kashe kuma aka kwantar da wasu da dama asibiti, yayin da cutar ta ɓarke a sansanin ‘tubabbun ‘yan Boko Haram’ a Maiduguri, babban birnin Jihar Yobe.

Gwamnatin Jihar Barno ta tabbatar da ɓarkewar cutar da kuma kisan da ta yi a sansanin ‘tubabbun’yan Boko Haram’ da ke Kosheri, kan hanyar Maiduguri zuwa Dikwa. Sannan kuma gwamnatin ta ce da yawan mazauna sansanin sun kamu da ciwo, ana kuma ba su magani da kulawa.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa waɗanda su ka mutu za su kai mutum 20.

“Ina tabbatar maka wannan cuta ta ɓarke a ranar Juma’a, inda a ranar mutum 14 su ka mutu”. Haka dai majiyar ta shaida wa wakilin mu, wanda kuma majiyar jami’i ne.

Majiyar PREMIUM TIMES da ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce wasu mutane shida sun mutu a ranar Asabar.

Cutar kwalara ta ɓarke a sansanin ‘tubabbun ‘yan Boko Haram’, har ta kashe biyu, wasu na kwance asibiti.

Aƙalla mutum biyu cutar kwalara ta kashe kuma aka kwantar da wasu da dama asibiti, yayin da cutar ta ɓarke a sansanin ‘tubabbun ‘yan Boko Haram’ a Maiduguri, babban birnin Jihar Yobe.

Gwamnatin Jihar Barno ta tabbatar da ɓarkewar cutar da kuma kisan da ta yi a sansanin ‘tubabbun’yan Boko Haram’ da ke Kosheri, kan hanyar Maiduguri zuwa Dikwa. Sannan kuma gwamnatin ta ce da yawan mazauna sansanin sun kamu da ciwo, ana kuma ba su magani da kulawa.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa waɗanda su ka mutu za su kai mutum 20.

“Ina tabbatar maka wannan cuta ta ɓarke a ranar Juma’a, inda a ranar mutum 14 su ka mutu”. Haka dai majiyar ta shaida wa wakilin mu, wanda kuma majiyar jami’i ne.

Sai dai kuma a martanin da Gwamantin Jihar Barno ta fitar a ranar Asabar, ta ce mutum biyu kaɗai su ka mutu, ba mutum 20 ba.

“Mutum biyu kaɗai cutar kwalara ta kashe daga cikin waɗanda aka auna aka tabbatar sun kamu da cutar a sansanin ‘tubabbun ‘yan Boko Haram’ da ke Kosheri”. Inji Kwamishinar Harkokin Mata, Zuwaira Gambo, kamar yadda ta shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Asabar.

“Sauran waɗanda aka samu da cutar kuma tuni an gaggauta cire su daga sansanin, an killace su wani wuri daban.”

Kwanan nan dai Hukumar Sojojin Najeriya ta ce aƙalla Boko Haram 70,000 ne su ka miƙa wuya tun daga watan Yuni na bara.