Buhari ya umarci jami’an tsaro su kara ƙaimi wajen ceto fasinjojin jirgin kasa dake tsare hannun ‘ƴan bindiga

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umurci jami’an tsaro da su kara kai kaimi wajen ceto fasinjojin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja-Kaduna.
Idan ba a manta ba a watan Maris ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.
Acikin makon jiya ‘yan bindigan sun sako mutum 11 bayan Sheikh Ahmad Gumi ya saka baki.
Kafin hakan a baya ‘yan bindigan sun sako mutum biyu daga cikin mutanen daga ciki akwai mata mai ciki.
Kakakin fadar shugaban kasa ya shaida cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar nan su gaggauta ceto sauran mutanen dake tsare hannun ‘yan bindigan.
“Gwamnati ta dauki matakai da za su taimaka wajen ganin ta ceto duk fasinjojin jirgin kasan dake hannun ‘yan bindiga.
“Maharan sun bukaci gwamnati ta sako mutanen su inda bayan gwamnati ta sako su sai maharan suka saki mutum 11 a maimakon duka fasinjojin dake hannun su.
A dalilin haka dole gwamnati ta maida hankali da kuma kara tamke damara don ganin sun dawo da sauran dake tsare gidajen su.