Buhari ya naɗa Kingibe Jakadan Yankin Tafkin Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe muƙamin Jakada na Musamman a Chadi da Yankin Tafkin Chadi.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

“An naɗa wannan muƙamin ne biyon bayan ƙudirorin da aka cimma a taron Kasashen Yankin Tafkin Chadi kan Makomar Kasar Chadi, wanda aka gudanar a ranar 25 Ga Mayu.

“Aikin Jakada na Musamman a Chadi da Tafkin Chadi, shi ne kula da lamurran da ke faruwa a Chadi da Yankin Tafkin Chadi.

“Kuma zai sa ido da kula da kuma sasantawa da ganin an maida ƙasar Chadi bisa turbar tsarin dimokraɗiyya, a ƙarshen wa’adin wannan gwamnatin riƙon-ƙwarya ta sojojin Chadi.

“Zai riƙa aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran ƙasashen ƙungiyar yankin Tafkin Chadi domin dawo da bunƙasar yankin, wanzar da zaman lafiya da kuma inganta tsaro.” Inji sanarwar wadda Boss Mustapha ya fitar, a ranar Litinin a Abuja.

Ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya ɗora wa Kingibe waɗannan ayyuka bisa yaƙinin cewa zai yi habbosa wajen ganin ya yi amfani da wannan dama domin a samu wanzuwar dawwamammen zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.