Buhari ya karbi wayar farko da aka kera a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi wayar selula ta farko da aka ce an kera a Najeriya, mai suna ITF Mobile.

Ministan Masana’antu, Cinikayya da Bunkasa Jari Adeniyi Adebayo ne ya damka wa Buhari wayar, kafin su fara Taron Majalisar Zartaswa tare da sauran Ministoci.

Minista Adeniyi ya ce wayar wadda aka damka wa Shugaba Buhari daya ce daga cikin wayoyi 12 da Sashen Koyon Fasahar Lantarki da Kayan Wuta na Cibiyar ITF su ka kera, ta hanyar amfani da kayan da aka samar a cikin Najeriya.

“An kaddamar da samfuran wayoyi har 12 da wannan cibiya wadda ke karkashin Ma’aikatar Masana’antu, Cinikayya da Bunkasa Jari.

Bayan kaddamar da wayar wadda Buhari ya karba da hannun sa, an kuma rantsar da Kwamishina daya a Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa da kuma wani Kwamishina din ga Hukumar Kula Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC), kafin a fara taron Majalisar Zartaswa.

Buhari ya Shugabanci taron Majalisar Zartaswar a Dakin Taron Ofishin Aisha Buhari.

Mataimakin Shugaban Kasa da wasu Ministoci sun hallara. Sauran Ministoci kuwa daga ofis din su kowane ya halarta ta talbijin.