Ƙungiyar ASUP ta janye yajin aiki

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Ƙungiyar nan Malaman ƙwalejojin kimiyya da fasaha (Acadamic Staff Union of Polytechnics, ASUP) ta sanar da janye yajin aikin da ta shafe watanni tana yi bayan ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya.

Ƙungiyar ta sanar da janye yajin aikin ne a wata sanrwa da ta fitar a ranar Laraba ɗauke da sa hannun Magatakardar ta na ƙasa, Shammah Kpanja.

ASUP ta shafe kwanaki 65 tana yajin aiki wanda hakan yayi sanadin ajiye ɗalibai a gida na tsawon wannan lokaci.

A cikin takardar da sanarwar, ƙungiyar ASUP ta ce ta janye yajin aikin ne na tsawon watanni uku kafin nan gwamnati ta aiwatar da dukkan buƙatocin dake rubuce a cikin takardar yarjejeniyar da gwamnatin ta sa hannu da ƙungiyar.