BAUCHI: Dole ‘yan Acaba su bi doka daga yanzu ko su kuka da kansu – Hukumar BAROTA

Hukumar kula da kiyaye dokokin hanya na jihar Bauchi BAROTA ta bayyana cewa za ta karfafa dokar hana ‘yan achaba a jihar.

Shugaban hukumar Tijjani Gamawa ya sanar da haka wa manema labarai a garin Bauchi.

Ya ce hukumar za ta tabbatar da ganin dokar na aiki yadda ya kamata a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Maris 2020 gwamnati jihar Bauchi ta kafa dokar hana ‘yan achaba a jihar domin dakile yaduwar cutar korona.

A dalilin haka Gamawa ya ce hukumar za ta kama duk dan achaban da ya dauki fashinja fiye da mutum daya a babur ko kuma duk wanda ke tukin gangancin da babur a jihar.

Sannan kuma shugaban hukumar ya gargadi masu Keke Napep da su daina daukan fashinja a gaba.

Gamawa ya ce gwamnati ta yi hakan ne domin samar da tsaro a fadin jihar.

” Duk mai keken da muka kama ya dauki fasinja a gaba za mu kwace keken sa sannan za mu ci shi tara kuma mu maka shi kotu.

Ya kuma yi kira ga masu Keke musamman baki da suka shigo jihar daga wasu jihohi da su yi rajistan kekunan su domin gane yawan mutanen dake shiga da fitan a jihar.

Ya kara da cewa hukumat ta kama mutum sama da 100 da suka karya dokar hanya a jihar, sannan an kore masu tireda da suka kakkafa kananan shaguna a wuraren da bai kamata a fadin jihar.

Gamawa ya ce zuwa yanzu hukumar za tashi ‘yan kasuwan dake kasuwanci a Area Office, ma’aikatar Aiyuka, kusa da kasuwar Muda Lawal zuwa wani wuri dabam.

Ya ce bisa ga umurin gwamnan jihar Bala Mohammed za a tashi ‘yan kasuwan ne saboda kawu cinkoso a hanyoyin da suke kasuwanci a kai domin motoci su samu walwalar zirga-zirga.