Ba mu yi alƙawarin yin hadin guiwa da PDP a zaɓen gwamnan Kaduna ba, kowa tasa ta fisshe shi kawai – In ji Jam’iyyar NNPP mai kayan daɗi

Jami’yyar NNPP mai alammar kayan daɗi a jihar Kaduna ta bayyana cewa bata yi tsari na hadin gwiwa da jami’yyar PDP ba a zaben gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki da z aa yi ranar 18 ga Maris ba.
Mai bai wa jami’yyar shawara kan harkokin shari’a Ibrahim Ahmed ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Laraba a garin Zaria.
Ƴan takaran gwamna su tara a jihar Kaduna sun janye daga takarar su domin mara wa PDP baya a zaɓen gwamna dakr tafe.
‘Yan takaran sun fadi haka ne a karkashin inuwar kungiyar ‘ of ‘Kaduna State Rescue and Rebuild Gubernatorial candidates Forum’ inda suke bayyana adawar su da tikitin tsayawan takarar Musulmi da Musulmi suna mai cewa an shirya shine domin raba kan mutane a jihar ta hanyar addini.
Sai dai kuma Jam’iyyar NNPP ta gargaɗi mutanen jihar Kaduna da su tabbata ba su zaɓi APC domin jiki magayi.
Ahmed ya ce shigo da siyasar addini da aka yi a siyasar Kasar nan zai iya dawo da cigaban da aka samu a shirye yasa baya.
Ya ce jami’yyar NNPP ko ta jihar ko ta kasa da kwamitin aiyukka ta jami’yyar ba su da masaniya kan hada gwiwar da aka Yi.
Ahmed ya ce kamata ya yi jami’yyar ta dauki wasu matakai kafin ta damka kanta ga hadin gwiwa amma hada gwiwa ba na mutum daya bane ko na wani dan takara ba.
Ya Yi kira ga mutane da sauran mambobin jami’yyar da su kira domin su ji bayani daga wajen jami’yyar idan har tana da niyar yin hadin gwiwa da kowace jami’yya.