Matawalle ya ware Naira miliyan 70 don tallafawa masu sana’ar POS 300 a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ware Naira miliyan 70 domin tallafawa masu sana’ar cire kuɗi da aikawa da kuɗi ta hanyar POS 300 a jihar.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Yazeed Danfulani ya sanar da haka a waken taron raba wa matasa mata da maza 300 na’urar POS da aka yi a garin Gusau a cikin makon jiya.
Danfulani ya ce gwamnan ya yi haka ne domin inganta matasa ta hanyar mai da su masu cin gashin kansu.
“Za a baiwa kowani matashi setin kujeru, tebura, shago, na’urar POS da jarin Naira 50,000 da za su fara sana’ar da su.
Danfulani ya ce gwamnati za ta kafa kwamitin sa Ido domin tabbatar da ganin matasan sun yi amfani da kuɗaɗen da aka basu domin sana’ar POS.
Ya Yi kira ga matasan maida hankali sannan su yi amfani da wannan dama domin bunkasa kansu a jihar.