Ba abu mai sauƙi bane riƙe ma’aikatar gona- Sabo Nanono

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Tsohon Ministan Harkokin gona da Raya Karkara Mohammed Sabo Nanono ya ce ba abu ba ne mai sauƙi riƙe ma’aikatar gona.

Ya ce ma’aikatu masu zaman kansu na matuƙar taimaka wa wajen mayar da aikin ma’aikatar mai wahala.
Nanono ya bayyana hakan ne yayin miƙa al’amuran ma’aikatar ga sabon Ministan, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, wanda ya gudana a Abuja.

Ba abu mai sauƙi bane riƙe ma’aikatar gona- Sabo Nanono
Zan kasance shugaba da za a riƙa tunawa da shi da ya daidaita Najeriya – Buhari

A cewar sa, “A wuri na ba abu ba ne mai sauƙi. A matsayina na wanda ya taba aiki a ma’aikata mai zaman kanta, dole a riƙa samun sabanin muradi a ma’aikatun gwamnati a nan da can. Amma a ƙarshe mun fahimci juna da su.”
Ya ci gaba da cewa, “Muna da babban ƙalubale a wannan ma’aikatar domin idon kowa na kan mu. Dan tashin farashin kaya sai a ce ma’akatar noma ce, abinci, komai dai aka samu matsala. Duk da haka mun karbi wannan ƙalubale, amma fatana shi ne wata rana ma’aikatar za ta kasance mai magana da murya ɗaya.”

Share The News

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaZan kasance shugaba da za a riƙa tunawa da shi da ya daidaita Najeriya – Buhari

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.