AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Mahara sun kashe Hakimin Gada, sun yi wa mata fyaɗe a Zamfara

‘Yan bindiga sun kutsa garin Gada da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bunguɗu, inda su ka kashe Hakimin Gada, Umaru Bawan-Allah da wasu mutane uku.

Sakataren Masarautar Bunguɗu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun shiga garin wajen ƙarfe 1 na dare, inda su ka riƙa banka wa kayan abinci wuta.

Sakataren ya ce za a yi jana’izar Hakimin Gada a yau Laraba misalin ƙarfe 4 na yamma.

Wakilin mu ya ji cewa ‘yan bindigar sun daɗe sosai a cikin garin su na shuka rashin mutunci, tare da yi wa mata fyaɗe gadan-gadan.

An kashe Hakimin Gada da ke da tazarar kilomita bakwai da Bunguɗu, watanni uku bayan ‘yan bindiga sun kama Bunguɗu, wanda ya shafe kwanaki 33 a hannun su, kafin su sake shi.

An kai wannan hari ne kwana huɗu bayan mahara sun fasa garuruwa 15, sun kashe mutum 7, sun kwashi matan aure da ‘yan mata 33 a Zamfara.

Mahara ɗauke da muggan makamai sun fafari ƙauyuka 15 a yankin Ƙaramar Hukumar Gusau cikin Jihar Zamfara.

A harin wanda su ka kai ranar Asabar, wato ranar Kirsimeti, sun kashe mutum bakwai kuma sun kwashi matan aure da ‘yan mata 33.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin BBC Hausa cewa, “ƙauyukan da ‘yan bindiga su ka shiga, har da Geba, Kura, Duma, Gana, Tsakuwa, Gidan Kada da Gidan Ƙaura.”

Ya ce tun “Asabar maharan ke bin ƙauyukan ɗaya bayan ɗaya da dare, har sai wajen asubahin wayewar garin Lahadi su na kai farmaki.”

Ya zuwa yammacin ranar Lahadi babu kowa a cikin kauyukan, saboda gudun kada maharan su sake koma masu.

A yanzu dai al’ummar garuruwan sun yi cincirindo a rukunin gidaje na Damba Estate da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

“Yan bindiga sun ɗauki mata 10 a Kura, sun kwashi mace 9 a Bayauri, cikin su kuwa har da ‘yan mata. Sun yi gaba da mata bakwai a Gana da wasu bakwai a Duma.

“A garin Kura ne su ka kashe mutum bakwai. Kuma har yanzu an kasa zuwa a ɗauko gawarwakin mamatan, saboda fargaba.”

Wani mazaunin kusa da Damba Estate, ya shaida wa wakilin mu cewa ya ga mutanen abin tausayi, a waje su ke zaune hululu, yawancin su duk mata da ƙananan yara ne, ga babu abinci babu komai. Kai ka ce babu gwamnati a ƙasar nan.”

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da an kai hare-haren. Amma ya ce sojoji sun fatattaki maharan a daidai lokacin da su ka shiga ƙauyen Geda.

Sannan kuma ya ce adadin garuruwan da ‘yan bindigar suka shiga bai kai 15 ba.

Wakilin mu ya kasa samun Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Zamfara.