ARCEWAR ƊAURARRU 5,238 DAGA KURKUKU: Ku kashe masu kai hari kurkuku har lahira – Umarnin Aregbesola ga Jami’an tsaro

“Kada ku tsaya harbin wanda ya kawo hari a kurkuku inda za ku lahanta shi. Ku harbe shi inda zai mutu farat ɗaya kawai.”

MInistan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bada umarni ga Jami’an Tsaron Gidajen Kurkuku cewa daga yau duk wanda ya nemi kai wa kurkuku hari, to a bindige shi har lahira.

Aregbesola ya yi wannan jawabi a ranar Litinin, yayin da ya kai ziyara Gidan Kurkukun Agodi da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

A wannan kurkuku ne ɗaurarru 837 su ka tsere a ranar 23 Ga Oktoba, 2021. Daga baya Minista ya ce an kamo 262 a cikin su.

Aƙalla ɗaurarru 5,238 ne su ka gudu daga gidajen kurkuku daban-daban na ƙasar nan, a cikin shekarar 2021.

“Daga yau ba za a sake zuba ido wasu ɓatagari na kai wa gidajen kurkuku hari ba.

“An ba ku umarni daga yau ku bindige duk wani ɓatagari da ya yi yunƙurin kai hari a gidan kurkuku.

“Kada ku tsaya harbin mutum inda za ku lahanta shi, ku yi saiti ku harbi inda zai mutu murus, nan take.

“Kurkuku wuri ne na tsaro, na gwamnatin tarayya, wanda bai kamata a riƙa yi masa wasarere ba. Don haka kada ma ku bari ana matsowa kusa da kurkuku.” Inji Aregbesola.

Daga nan ya nuna damuwa a kan cinkoson ɗaurarru da tsararru a gidajen kurkuku na faɗin ƙasar nan.

Ya ce gwamnatin tarayya na nan na lissafa sunayen waɗanda za a rage, musamman waɗanda su ka shafe tsawon shekaru ba a yanke masu hukunci ba. Kuma ko da an yanke masu hukuncin, to ba za su yi zaman wa’adin da ya kai wanda su ka yi kafin a yanke masu hukunci ba.

Ya buga misali da ɗaurarru 1001 da ke kurkukun Agodi, amma 400 ne kaɗai aka yanke wa hukunci, sauran duk tsawon zaman yanke hukunci su ke yi.

Haka kuma Aregbesola ya nuna damuwa kan tsadar ciyar da ɗaurarru a gidajen kurkuku. Shi ma ya ce gwamnati na nan na ƙoƙarin rage matsalolin.